Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

KAJI ABINDA: MESSI YACE GAME DA RONALDO-(Karanta-)

$
0
0

          Ronaldo Gwarzon Dan Kwallon Kafa Ne-Messi.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

              Ronaldo Gwarzon Dan Kwallon Kafa Ne-Messi

Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona, Lionel  Messi ya bayyana takwaransa na kungiyar Real Madrid, Cristiano Ronaldo a matsayin daya daga cikin gwarazan kwallon kafa da duniya ta ke da su a yau

 

Bayan dogon yabo da ya yi ga Ronaldo, Messi ya bayyana cewa babu wata gaba ko adawa a tsakaninsa da Ronaldon kamar yadda ake hasashe

 

Messi ya bayyana cewa mutane na ganinsu a matsayin abokan adawa ne saboda kasancewarsu na manya ‘yan kwallon kafa biyu da suka taka leda a manyan kungiyoyi biyu na Spanaiya da ke adawa da juna wato kungiyoyin Real Madrid da Barcelona

 

A baya-bayan nan ‘yan wasan biyu sun musanta batun wai akwai adawa a tsakaninsu, inda aka jiwo Cristiano Ronaldo na cewa akwai “danganta mai kyau” a tsakaninsu kuma yana jin dadin kallon Messi yana taka leda

 

Shi ma Messi a nasa bangaren ya yi yabo ga Cristiano Ronaldo tare da bayyana shi a matsayin zakakurin mutum da a kullum ya ke da burin ya ga ya yi nasara

 

“Batun wata gaba ko adawar da ke tsakanina da Ronaldo kirkirar ‘yan jarida ce, amma babu ita a zahiri” Messi ya ce ga kafar Tencent Sports

“Abinda ya ke shi ne muradinmu shi ne na mu yi aiki tukuru a kowace shekara, mu yi wa kungiyoyinmu kokarin samun nasara a wasanni, banabada muhimmaci ga labaran da ke fitowa daga waje”

“Ronaldo, dan kwallon kafa ne na ban mamaki wanda kwazonsa ke dada bayyana shekara bayan shekara. Wannan ne ma ya sanya ya zama daya daga cikin gwarazan ‘yan kwallo da duniya ke alfahari da su a yau”

The post KAJI ABINDA: MESSI YACE GAME DA RONALDO-(Karanta-) appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>