WASU ABUBUWANDA MATA KEYI DOMIN MAZA A NAJERIYA
Soyayya ta zama kamar yaki yanzu a Najeria, kowa yana dagewa wajen neman Soyayya. A wannan kasar tamu mai dauke da kimanin Mutane Miliyan 150 zakayi tunanin samun masoyi abune mai sauki wannan kuma ba hakan bane. Neman Soyayya ta gaske abune mai wuya sossai, musamman idan zaka duba Addini, Yare, da sauransu.
Mutane da dama suna aikata abubuwan ban mamaki domin neman Soyayya musamman Mata, misali anan shine:
1.Saka Duwawun Karya.
Maza da dama a Najeriya suna sha’awar mata masu Manyan Baya, wanda shiyasa mata suke sayen wando mai hade da soso domin kara musu girman Bayan su.
2. Canza Launin Fata daga Baka zuwa Fara.
Abu na biyu shine yadda mata suka shiga shafe shafen Mai, da anfani da sabulan wanka masu canza launing fata. duk wannan yakan farune domin mata sun fahinmi maza da dama na son fararen Mata.
3. Karin Girman Jiki da Kuma Rage Jiki.
Idan aka zo ga asalin neman abokin zama zaka samu wasu maza sunyi so su auri mata marasa Jiki wasu kuma sunfi sha’awar masu jikin. wannan yasa mata masu jikin suke kokarin rage Kiba domin masoyinsu baya son su da kiba kokuma yafison mata sirara, haka zalika mace marasa jiki zata nema yin kiba domin ta kasance irin wadda masoyinta yake so ta zama.
zakaga sun fara ciye ciye domin neman kiba ko kuma zama da yunwa domin su rage Kiba.
4. Saka Hips din karya.
Yan mata da dama yanzu sun maida saka Hips din karya ado domin kuwa yanzu ya zama ruwan dare a kasuwa. A kullun suna shago wajen sayen Wando mai dauke da Hips domin su rika jan ra’ayin yan maza masu sha’awar Hips.
The post WASU ABUBUWANDA MATA KEYI DOMIN MAZA A NAJERIYA appeared first on MUJALLARMU.