Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta sanar da kammala zabar mutane guda 200,000 da ta dauka a aiki a matsayin kashin farko na shirin N-power wanda ta kaddamar ‘yan watannin da suka gabata. Mutanen sun kunshi kaso 40 daga cikin adadin da gwamnatin ta ce za ta dauka tun farko.
A karkashn shirin, gwamnatin za ta dauki ma’aikata guda 500,000 da suka hada da malaman makaranta da kuma ma’aikata a wasu bangarori na musamman.
Mai magana da yawun mataimakin shugaban Nijeriya Yemi Osinbajo, Laolu Akande shi ya sanar da hakan aranar juma’ar da ta gabata, inda ya bayyana cewa an zabo ma’aikatan ne daga kowacce jaha a kasar nan, tare da kulawa ta musamman da aka baiwa yankin arewa maso gabas
Yanzu haka dai ana kan tantance ma’aikatan, kuma ya bayyanan cewa da zarar an kammala, za su fara aiki.
Haka kuma ya kara da cewa gwamnatin na ci gaba da shirye shiryen cika alkawarin daukar sauran mutane 300,000
via alummata.com