Ma’anar Assīratu: A Larabci tana daukar ma’anar hanyar ko tafarkin mai kyau ko mara kyau, kuma tana daukar ma’anar halaye na
mutum. Amma a zaurancen Malaman tarihi tana nufin: Abin da aka ruwaito na rayuwar Manzon Allah (s.a.w) tun kafin haihuwarsa har ya zuwa wafatinsa. Wanda hakan ya kunshi abubuwa kamar haka:
1. Haihuwarsa da nasabarsa da danginsa
2. Tasowarsa da kuruciyarsa da samartakarsa da rayuwarsa da
al’ummarsa kafin wahayi ya sauko masa
3. Saukar wahayi a gare shi
4. Dabi’unsa da yadda yake tafiyar da rayuwarsa
5. Mu’ujizozinsa da Allah ya karrama shi da su
6. Tsarin da’awarsa ta Maka da Madina
7. Yadda ya mu’amalanci Mushrikai da Yahudu da Munafukai da Kiristoci da wadanda suka yi imani da shi
8. Yakokinsa
9. Siyasarsa.
Fa’idar Karanta Tarihin Annabin Rahama. Karanta tarihin Annabi (s.a.w) yana da yawa, daga cikinsu akwai:
1.Sanin Allah
2. Samun tsarin zamantakewar rayuwa tsaftatacciya mai dadi
3.Sanin yadda ake tafiyar da Al’umma
4. sanin yadda za a tafiyar da makarantu da ma’aikatu
5. Juriya da jajircewa akan manufa
6. Salon koyarwa da ladabtarwa da tarbiyyantarsa
7. Sanin hanyar tattalin arziki da bunkasa shi da tsaro
8. Samun kyawawan halaye
9. Nutsuwa da zurfin tunani
8. Samun shiriya
9. Yadda ake zama da abokin adawa
10. Tarihin Manzon Allah (s.a.w) ya zo ya fitar da Mutane daga duhun jahilci zuwa haske na ilimi
11. Samun karuwar imani
12. Koyi da Manzon Allah (s.a.w)
13. Zamantakewar iyali
14. Sanin hakkin bil Adama da Aljanu da Dabbobi…Kai rayuwar Manzon Allah (s.a.w) kowa zai dau darasi a ciki Shugaba ne, ‘Yankasuwa ne, Manoma ne, Makiyaya ne, mai Mulki ne, da dai sau ransu.
Aliyu Namangi Allah ya yi masa rahama ya ce:
Dan Amina mafi darajja,
Da waninsa mijin Hadija,
Rabbana ya baka hujja,
Wadda ba ta ga mai darajja,
Wani in ba kai ba dan Suwaiba .
Mu hadu a darsasi na 3
Nuhu Ubale Ibrahim
(Abu Abdilhalim)
Litinin: 07/11/2016.
Zaka iya Karanta Kashi na Daya DAUSAYIN NI’IMA TARIHIN ANNABIN RAHAMA KASHI NA DAYA