Arewacin Nigeria ya kasance wata matattara ta yan ta’adda masu cin Karen su ba babbaka. Wadanda karfin su har ya kai ga kafa tasu daula ta daban acikin wasu sassa na arewacin Nigeria.
Rashin daukar matakai da yin Ko oho akan sha’anin tsaro na gwamnatin data gabata, yana daya gada cikin shika-shikan faruwar ta zabe a wancen lokaci. Hakan yasa talakawa sukayi tsayin daka domin ganin sun canza tsohuwar gwamnati zuwa sabuwar gwamnati, abisa amanna dacewa zasu samu tsaro da saukin rayuwa.
To sai dai harwayau munanan ‘yargidan jiya, duk dayake alokacin da sabuwar gwamnati ta baba buhari tana cikin zafin ta, ta’addanci da tashe-tashen bomabomai ya lafa a arewacin Nigeria.
Sai dai a kwanakin nan bamusan Ina aka dosa ba. Ta’addanci ya dawo da wani sabon Salo, tahanyar yiwa jarumai kuma zaratan sojojin Nigeria dauki dai dai.
A jahar Zamfarama, duk da tulin sojojin da aka tule muna, amma shekaranjiyar nan anyiwa sama da mutane arba’in kisan gilla a karamar hukumar mulki ta maru. Tashe-tashen bomabomai sunfara dawo wa a wasu garuruwa dake cikin garin Barno.
Idan mukayi la’akari da wadannan tashin hankula dake kokarin dawowa a dai dai wannan lokaci, zamu iya cewa Har wayau muna nan yargidan jiya.
Yakamata gwamnatin Nigeria ta kara karkato da hankulan akan sha’anin tsaro sama da yanda ta karkata akan sha’anin bincike.
Via Zayyanu Maigishiri Gusau