DAGA TASKAR TARIHI…
Alaka tsakanin Kano da daular Saudiyya alaqa ce mai tsaho da dimbim tarihi. Addinin Hausawa dai, addini ne daya samo asali daga Daular ta Saudiyya. Kusan ma iya cewa, babu wani mutum da yake da daraja a idon Bahaushe a duk fadin duniya irin Balarabe. Dalilan hakan sun hada da cewa harshen Larabci harshen Annabi ne (S.A.W) ne kuma Larabawa yan’uwan Annabi (S.A.W) ne. Hausawa a gurin su ba daraja irin a ce a cikin nasabar ka kana da alaqa da larabci, ko kana da ilimi a cikin harshen.
Tarihin zamantakewa tsakanin wandannan al-ummai biyu ya fara ne, ma iya cewa daga zuwan Shehu Muhammad al-Maghili kasar Kano. Shehu al-Maghili kamar yadda Masana suka rawaito ya zo ne daga Madina sakamakon mafarki da ya yi da Annabi (S.A.W) da ya ce masa ya taho yamma ya yada addinin Musulunci. Shehu al-Maghili ya debo kasar garin Madina ya taho da ita yana gwadawa da kasar duk garin daya sauka. Ba ta yi daidai da kasar ko ina ba sai ta Kano inda hakan ya nuna masa cewa nan ne Annabi (S.A.W) ke nufin sa da zuwa! Shehu Maghili ya zo Kanon a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499), in da har ya rubuta wa Kano littafin “Taj al-Muluk”, wanda ya zama kundin tsarin mulkin ta na farko. Zuri’ar sa sune, har yau suke riqe da sarautar Sarkin Sharifai, a fadar Kano.
Tun daga nan, kofa ta budewa Larabawa, musamman na Afirka ta Yamma inda Kano ta zama cibiyar su ta tallan haja da Addini da Akida da Ala’adu musamman daga farkon karni na sha biyar, inda kasar Hausa ta fara cin moiriyar Trans Saharan Trade. Litattafan Addini na Mazhabar Malikiyya, wadda Mazhaba ce ta Madina, su ka fara bulbulowa kasar Kano. Ilimi ya kara yaduwa, Kano ta kara tabbatar da matsayin ta a cikin garuruwan Musulunci!
Mutanen kasar Hausa sun fara zuwa kasar Saudiyya tun tsahon lokaci. Tun suna zuwa a kafa da taimakon dabbobi, har zuwa karni na sha tara da Bature ya kawo musu mota da jirgin sama. Tafiyar tana daukan kamar shekaru biyar a matsakaicin lissafi. Wasu matafiyan na rasuwa a hanya, wasu kuma sukan yada zango a Sudan, ko Misra, wasu kuma igiyar ruwa ta kada su Yemen. Bisa kiyasi, idan mutum Ashirin suka tafi, wadanda ke dawowa ba sa fin biyu ko uku. Zuwan Jirgin saman Turawa ya saukaka hakan, in da dubban mahajjata ke tafiya, kuma baifi ace goma sun rasu ba. Sarkin Kano Abdullahi Bayero, shine a shekarar 1934 ya fara zuwa kasar Saudiyya don sauke farali a jirgin sama.
Hausawa sun taka rawar gani a Daular Saudiyya, kama daga kafa daular da Ahalin Abdallah Saud su ka yi har ya zuwa yau. A shekarar 1803 da mabiya bayan Sa’ud suka kawo hari na farko Makkah domin kwace ta daga hannun Sharif Hussaini, Hausawan mu goyon bayan su ya rabu biyu, wa su sun goyawa Sharif Hussaini baya, wasu kuma sun goyawa Ahl Saud. Koma dai ya abin yake, bayan kafa daular, Hausawa sun sami martaba a idon duka bangaroron biyu. Martabar Hausawa a idon sabuwar Daular Saudiyya, ta kai shaidar Hausawa ba a haufi a kanta a tsakanin mahukuntan kasar ta Saudiyya.Tsahon lokaci mafi yawan sana’ar Hausawa a kasar Saudiyya baya wuce dinki, siyar da gwajo, girki, siyar da abinci, gadi, sana’ar chanji, awon kaya a filin jirgi, tukin mota, aikin kamfani, Leburanci da sauran sana’o’i masu tarin yawa. Ko da yake akwai tsirarun yan Najeriya a Saudiyya da suke da karatun zamani, dokokin Saudiyyan kan zamar musu matsala wajen samu aiki.
Wani abun takaici shine, a lokacin mulkin Sarki Faisal, ya yi yunkurin tantance yan kasa da baki, kuma aka sanar cewa dukkan mai son zama dan Kasa yaje ya karbi takardar, kyauta. Abin dariya za a ace ko alajabi, wani Takari da yake bani labari, yan Najeriya har Allah ya isa suka dinga yiwa yayan su idan suka karbi takardar. Fafur, tamkar jarumin da yake kai naushi dan gudun mutuwa, suka rufe ido suka ki karbar izinin zama yan kasar. Kamar yadda jikokin wadanda hakan ta faru da su suka sanar dani a wani bincike, hatta wani mutum da ya dinga goya jakar takardun a bayan sa ana zaga unguwanni da shi a Makkah, ana bin gida-gida ana tallan takardar, har ya mutu ba shi da ita! Da kyar da jibin goshi jikan sa, bayan shekaru, ya samu! Wata qila hakan na da nasaba da talaucin da kasar ta Saudiyya take ciki a wancan lokacin, wanda hakan ya sa Yan Najeriya jin cewa kasar su tafi arziki, saboda haka ibada kadai ke kai su Saudiyya, ba zama ba. Yau gashi yan Najeriya na neman takardar da kudin su, ana wulakanta su. Uhm! Duniya juyu juyi, wai kwado ya fada ruwan zafi!
Rashin wannan takarda yasa yanzu Yan Najeriya suna cikin mafi yawan masu zaman da ake kira zaman shahada, wato zaman ba bisa ka’ida ba. Hausawan da ke da mutunci kwarai a idon mahukuntan Saudiyya, wanda a da can yarda ta sa suke aiki a gidan kudi, a dora musu buhunan kudi su kai ma’aikata su kadai, yanzu kudin su ma abin tuhuma ne, balle wani ya basu na shi amana. Dama dai wanda ya ki sharar Masallaci, ai dole zai yi ta kasuwa.
Duk da wannan tsohuwar alaka, abin takaici ne ace babu wata yarjejeniyar kasuwanci a tsakanin wadannan kasashe biyu. Babu wata doka da take bawa dan Najeriya kariya akan kasuwancin sa a Daular ta Saudiyya, haka zalika wadda za ta karfafawa yan Saudiyyan kwarin gwiwar kafa kamfanoni a Najeriya. Kasashen da Najeriya ta kulla wannan yarjejeniya da su kamar Kasar Sin da Amurka, alaqarsu bata kai tsufan ta Saudiyya da Najeriya ba. Wannan yasa wadanda suke son gudanar da halastaccen kasuwanci da zai kunshi kudade masu dimbim yawa ke fuskantar barazanar rashin kariyar diplomaciyya ga dukiyoyin su. Hakan na da hadari kwarai da gaske, duba da yanda yanzu yan Najeriya ke fuskantar rushewar martaba a hannun mahukunta da mutanen Daular ta Saudiyya.
Akwai bukatar gwamnati ta maida hankalinta kwarai wajen yin wannan yarjejeniya, domin da yadda Kasar Saudiyya ke bajakolin aqidar ta ta addini, a Arewacin Najeriya, cinikayya ta ke haka, da kwarai talakawan Arewa sun amfana. Yarjejeniyar kuma zata saukaka harkar Kano-Jidda wadda ke addabar mahukutan Saudiyya, da safarar mutane da ake, wanda hakan ke kara zubarwa da mutanen Najeriya mutunci a idon duniya.
Abu na karshe, ya kamata gwamanti ta dubi barazanar karyewar Naira da yan kasuwar Najeriya suke fuskanta a kasar ta Saudiyya da idon rahama domin babu dalilin kyale wannan kasuwanci mai dimbin tarihi ya rushe. Akwai matsala babba, idan aka ce akida kadai mutanen Arewa ke amfana da Daular Saudiyya, domin idan aka duba batun da kyau, za a ga kusan babu in da Najeriya ta ke morar Saudiyya, in banda ta fuskar ilimi, ilimin ma na siyasar akida. Alakar kuwa ta wuce a barta iya haka, musamman a wannan zamani da kasuwanci ne ginshikin alaku.
Huzaifa Dokaji
(Dalibin Tarihi ne daga Jami’ar Bayero dake Kano)
Arabiandokaji@gmail.com 08135353532.