“LABARINMU A YAU, NA WASU JARUMAN SURUKAINE SU UKU” WANE SURIKI NE YAFI KUNYA ?
1) Wani surukine yaje gidan mahaifiyar matarsa (surukarsa), da zuwansa sai ya tarar ta gama girki kenan, ta fitar da garwashin wuta zata kashe.
Gogan namu bai kula ba, sai kuwa ya tsugunna kan wannan garwashin wutar yana gaida surukar tasa.
Haka ya daure har wutar nan ta mutu tana k’ona shi, amman don kunya ya kasa motsawa.
( DAMA LOKACIN SANYINE SAI ACE TA KWANA GIDAN SAUKI)
2) Shikuma wannan suruki haduwa yayi da mahaifin matarsa a hanya, sai ya tsugunna suna gaisawa.
Ashe bai san kunama ta shiga rigarsa ba, haka tayi ta harbinsa amman saboda tsananin kunya haka ya hakura ya kasa daukar wani mataki a kai.
3) Shi kuwa wannan jarimin namu, mota suka hau tare da surukarsa, sai kwandasta (karen mota) yayi irin janyo kofar nan don ya rufe, cikin rashin sa’a sai ya hada da yatsar surukin nan ya datse masa ita da murfin motar.
Azaba ta ishesa har ta kai jini na zuba daga yatsar.
Amman ko ihu ya kasa yi don ya samu mafita, saboda tsananin jin kunyar surukarsa dake motar nan.
http://rabswudil.tk/