Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

LABARINA: LABARIN WATA YARINYA MAI FARIN JINI

$
0
0

YADDA AKAYI NA SAMU FARIN JINI A WAJEN SAMARI

Alhamdulillahi Godiya ta tabbata ga Ubangijin Kowa da Komai

Ina godiya ga Iyayena da suka bani cikakkiyar tarbiya irin ta Musukunci, Domin kuwa ni nasan sun taimaka min wajen samun Ilimin Addini da na Boko Domin kuwa na samu Saukar AlQur’ani Mai girma, na fara Hadda kuma nayi nisa, kuma na samu na Gama Secondary School ina Jiran Admission zuwa Jami’a.

Akwai wasu abubuwa da dama da suka faru a rayuta da yasa nake mai godiya ga Allah (SWT) da iyayena da suka rene ni suka bani Tarbiya. Na kasance yar talaka kuma ni bakar mace ce kuma gajera, Alhamdulillah ina da kyau iya nawa, domin nasan maza da dama zasu ce niba kyakkyawa bace kodan rashin tsawo da bakina. Amma hakan bai hana in samu farin jini a wajen samari ba domin kuwa a duk lokacin da saurayi yace yana sona ni bana walakanta dan Adam amma da zarar na fahimci ba da gaske yake ba ko kuma dan Iska ne toh a lokacin zai iya ganin bacin raina. Saboda wasu maza da sun ganki yar talaka saisu rika tunanin zasu same ki ta hanyar sauki musamman idan zasu nuna miki duki.

Toh nidai Alhamdulilla a gaskiya gidan mu baa muna wannan tarbiyar ba, idan saurayina yamin alheri ko kyauta zan karba amma da zarar na fahimci cewa yayi ne don neman hadin kaina to tabbas ina iya jefa masa abunsa a fuska.

Wannan tarbiyar da rayuwar Gidan mu tasa Samari da dama suke ganin mutuncin gidan mu kuma na samu farin jinni sossai duk da yake da dama suna min kallon mummuna, Alhamdulillahi yanzu haka ina da masoya da dama wanda suje nemana da Aure.

Ranar wata kawara take min wannan tambaya cikin wasa da dariya “Wai ya akayi ne kike da farin jinni, idan akwai wani abu da ake sha ki bani nima in sha ko zan samu samari. Idan har baza ki bani  ba toh ki taimakamin da daya daga cikin samarin ki”

Da na tashi sai na bata amsa: ’’ Idan har kina so kiyi farin jinni wajen samari, to ki rike mutuncin ki, Sannan duk inda zaki tafi ki tabbatar kin rufe Jikin ki, In sha Allah yin haka zai sa ki samu farin jini”.

Dan Haka ina kira ga Yan mata da mu rike mutuncin mu, Kada mu bari shedan ya rude mu domin kuwa ni a fahimtar da nayi wa Maza basu son Mata da basu san kansu ba.

 

Zaka iya aiko mana da takaitaccen tarihin Rayuwar ka idan har akwai wani sako a cikin da kake so ya isa zuwa ga alumma. Allah dai ya taimake mu baki daya.

Zaka iya aikawa ta hanyar whatsapp 08034208823


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>