Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

Gwamnonin APC 9 Da Wasu Jiga-Jigan Jam’iyyar 100 Za Su Fice Daga Jam’iyyar

$
0
0

Alamu masu karfi sun bayyana kuma alamun na haska cewa wasu gwamnonin jihohin Nijeriya har guda 9 da aka zaba akan doron jam’iyyar APC za su fice daga jam’iyyar nan ba da jimawa ba

Ba ma kawai gwamnoni ba, hasashe na nuna cewar jam’iyyar APC za ta rasa wasu jiga-jigai a tafiyar jam’iyyar har sama da mutum 100 a fadin tarayyar Nijeriya

Koda yake dai sakataren jam’iyyar ta kasa, Alhaji Mai Mala Buni ya musanta rade-radin, amma jaridar New Telegraph ta fitar da rahoto kamar yadda ta samu labari daga wani ginshiki na jam’iyyar ta APC cewa, APC za ta rasa muhimmin goyon baya daga yankin yammacin Nijeriya (jihohin yarbawa) da kuma wani kaso mai tsoka na yankin arewa ta tsakiya

Wannan jigo na jam’iyyar APC da ya ki yadda da a fadi sunansa ya bayyana cewa, akwai matsala sosai a jam’iyyar sakamakon ji da wasu ke yi na an watsar da su yanayin yadda ake gudanar da al’amuran mulki a jam’iyyar da ma kasa baki daya.

Amma daga bangaren shi sakataren jam’iyyar ta kasa, Mai Mala Buni, ya tabbatar da cewa babu wata matsala a jam’iyyar ta APC, kuma ma dai shugaba Muhammadu Buhari da gwamnonin APC na tafiya a layi daya na siyasa ba tare da bangaranci ko wariya ko kyama ga wani ko wasu ba.

daga alummata.com

The post Gwamnonin APC 9 Da Wasu Jiga-Jigan Jam’iyyar 100 Za Su Fice Daga Jam’iyyar appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050