Na Danladi Z. Haruna
danladiharuna@gmail.com 08030764060
Sautin kida na tashi bugudum – bugudum. Ya gyara motar a wajen fakin. Cikin sauri dattijon nan da ke min bambami ya zabura kamar soja lokacin da aka ba shi umarnin harbi. Ya kama marikin kofar ya bude masa. Wani matashi ya fito sanye da wani dirkeken bakin gilashi da jaket kwat ruwan kasa. Dattijon na gaishe shi amma ko kallonsa bai yi ba, sai amsawa yake ciki-ciki.
Daya mutumin ya dube ni ya ce, “Ka yi hakuri, halin Malam Amadu sai shi, bari ya zo na roke shi ya kai fom din ka. Na amsa da “To madalla na gode.” Nan muka cigaba da hira, anan na nakalci sunansa Labaran, shi kuwa dayan sunansa Amadu.
Labaran shine maigadi, Amadu shine masinja, amma kankanba da shisshigin Amadu ya kwace duk ayyukan biyun. Ya hana Labaran sakat, ga girman kai ga kushe da sauran munanan dabi’u kamar yadda Labaran ke min korafi. Ni dai na yi zugum ina tunani, har Amadu ya dawo daga maularsa ya zauna. Da sa bakin Labaran ya bani fom din ziyara na cike ya tashi ya shiga. Jimawa kadan ya fito ya kalle ni cikin izza ya ce, “An ce ka shiga.”
Zuciyata na cike da mamakin halin wannan dattijo, shi dai ba wani mai fada a ji ba, ba wani babban ma’aikaci ba amma ya dorawa kansa girman kai fiye da kima. Na tabbata ko yanzu matsayina a aikin gwamnati ya wuce nasa. Domin kuwa mukamin babban direba ne da ni. Wato matakin albashi na bakwai. Shi kuwa mafi kololuwar masinja ko maigadi shine matakin albashi na hudu. Watakila ma shi bai wuce na biyu ko na uku ba.
Na shiga ofishin cikin sallama, wani sanyi ya ratsa tun daga kaina har kafafuna. Sannan kamshi ya doki hancina, kafafuna suka nutse cikin tattausan kilishi, babu shakka ofishin mulki ya fi na direbobi kyau nesa ba kusa ba. A kuryar kofar shigowa daga sama akwai wata tangamemiyar talabijin wadda ke nuna sassa dabam – dabam na ginin ofishin har da kofar shigowa. A fisge na dube ta, Labaran da Amadu na zaune suna kallon hanya. A raina na yi addu’ar Allah ya sa dai ogan bai ga zuwa na da abin da ya faru ba.
Na rusuna ina mai gaisuwa. Abin mamaki sai ya miko min hannu muka gaisa. ‘Wannan mutumin ya fi maigidanmu kirki’ na fada a raina.
“Yayi min waya ya ce kana tafe. Tun dazu ya kamata ka zo, me ka tsaya yi a hanya ne?” Na yi murmushi na ce, “Yallaɓai gosulo ga kuma abin hawan nawa sai a hankali.”
“Ina sakon?” Ya fada yayin day a miko hannunsa gare ni.
Na sa hannu na fito da takardun daga aljihun babbar rigata na mika masa.” Ya karɓa ya dudduba, sannan ya dube ni ya ce, “Komai yaji, ka fada masa zan yi nazarinsu duk abin da ake ciki zan kira shi.”
Na juya zan tafi ina mai masa sallama. “Ungo wannan ka sha mai.” Tun kafin na karɓa na ji murna ta kama ni. Na yi godiya. Na kuma juyawa zan tafi ya sake kirana, “Af, please ka ba wa masinja na wannan ya siyo min kati.” Na karɓa na fita.
Laraba: 23/11/2016.
MUSHA DARIYA: BIYAN BASHIN DADDAWAR KAUYE
The post BIYAN BASHIN DADDAWAR KAUYE Kashi Na biyu appeared first on MUJALLARMU.