YAUSHE NE, KUMA OJUKKU YA ZAMA BAZAMFARE??
A baya-bayan nan Matsalar da ta bullo ita ce a shirin daukar ma’aikatan N-Power da Gwamnatin tarayya ta bullo dashi dan rage yawan matasan dasuka kammala karatunsu ba suda aikinyi.
Tun bayan da aka kammala tantance daukar wadannan matasa aiki na N-Power tare da fidda jadawalin sunayen wadanda suka samu nasarar samun wannan gurbin aiki a jahar zamfara a keta faman ce-ce-ku-ce akan ta ya sunayen inyamurai (Igbo) suka mamaye gurabun yan asalin jahar zamfara.?
Namu dai a halin yanzu shi ne; ce-ce-ku-cen. Maganar gaskiya akwai bukatar Gwamnati tayi tsauraran Bincike akan yanda wadannan inyamuran ke samun takardar shedar zama yan asalin jahar wato (indigent certificate) kasancewar su a jahar su ‘yan arewa basu isa su samu wannan damar ba.
Dan haka muna kira ga hukumomin da abun ya shafa da su tashi tsaye wajen magance wannan matsalar da ta dade tana faruwa a jahar Zamfara.
Ukhashatu Abubakar Gusau
The post WASU YAN AREWA NA KORAFIN YAN KUDU SUN MAMAYE GURABEN SU A SHIRIN DAUKAR MAIKATA NA NPOWER appeared first on MUJALLARMU.