Kimanin mutane Arba`in akasamu nasarar kwatowa daga hannun barayi dasuka addabi alummar jahar zamfara.
Mutanen da`aka sace satin da ya gabata aranar litinin. Anbayyana cewar babu kudi ko fada tsakanin jami`an Gwamnati da barayin dasukayi garkuwa da wayannan mutanen, anyi amfani da sasanci na adalci tsanin Gwamnati da Barayin. inji Mataimakin Gwamnan jahar zamfara Malam Ibrahim Wakkala
Dayake karbar mutanen da aka sacen, Gwamnan ABDULAZIZ YARI ABUBAKAR, Ya godima Allah bisa nasarar da aka samu wurin ceto su. Ya yabawa kwamitin sasanci tsakanin barayin dakuma Gwamnati. Haka yayi kira ga jami`an tsaro da sarakuna akan tabbatar da adalci wurin hukunta alumma.
Gwamnan ya jaddada Neman goyon bayan kowane sashe na shugabanci, idan matsala ta sake faruwa bayan anyi alkawullah da yarjejeniya to zaa hukunta duk Wanda yakeda hannu ciki.
Ukhashatu Abubakar Gusau
The post ANSAMU NASARAR KARBO MUTANE ARBA`IN DAGA HANNUN YAN,TA ADDAR DASUKAYI GARKUWA DASU A SATIN DAYA GABATA. appeared first on MUJALLARMU.