Anbukaci gwamatin tarayya da ta bunkasa hanyoyin kudaden shiganta da kuma dinke barakar dake kawo silalewan kudade domin samun biyan ma’aikatansu akan lokaci.
Yunusa A. Hassan, wanda sakataren hulda jama’ane na jam’iyar APC a karamar hukumar AMAC, ya bayyana hakanne a lokacin da yake Karin haske kan kasa biyan albashin wasu jihohi duk da kudaden ga gwamnatin tarayya ke ware masu.
Ya kuma koka da cigaban watsalar da watsi da mahimman abubuwa da yakamata gwamnonin wasu jihohin su maida hankali, ya kuma bukacesu dasu gabatar da tsare-tsare da ayyukan farfado da tattalin arziki.
Daga Umar El-farooq Ahmed a Abuja Najeriya.
The post ANBUKACI GWAMATIN TARAYYA DA TA BUNKASA HANYOYIN KUDADEN SHIGANTA appeared first on MUJALLARMU.