Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

SHUGABAN KASAR KAMARU PAUL BIYA NA ZIYARAR KWANAKI BIYU A NAJERIYA.

$
0
0

A yaune shugaban kasar kamaru Paul Biya, ke yin zirayar kwanaki biyu a Najeriya, bayan amsa gayyatar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya kuma sami rakiyar matarsa Chantal da kuma manyan jami’an gwamnatin kasar ta kamarun.

Jawabin hakan na dauke ne da sa hannun mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara kan watsa labarai da hulda da jama’a, Femi Adesina, inda yace shugabannin zasu tattauna ne kan wasu matsalolin Najeriya da kasar ta Kamaru, tare da kulalliyar alakar hadin kai kan yakin da akeyi da kungiyar boko haram da kuma rikicin kan iyakoki harma da laifunkan da ake aikatawa.

A ajawabin nasa, yace ana sa ran cim wata sabuwar yarjejeniya bisa ga wanda yake akwai, kari da karfafa harkokin kasuwanci da tattalin arziki tsakanin kasar ta Najeriya da na Kamarun.
Umar El-farooq Ahmed daga Abuja tarayyar Najeriya.

The post SHUGABAN KASAR KAMARU PAUL BIYA NA ZIYARAR KWANAKI BIYU A NAJERIYA. appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>