Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari, ya jaddada aniyarsa ta kawo ƙarshen hare-haren da ake zargin makiyaya na kaiwa kan wasu al’ummomin ƙasar.
Yayin da yayi wata ganawa da ƙungiyar bishop-bishop ta Najeriya, CBCN, Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa tuni ya baiwa shuwagabannin hukumomin tsaro umarnin ɗaukar duk matakan da suka dace da kuma binciko duk wani mai hannu cikin wannan lamari.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, ”A shirye muke mu kare duk ‘yan Najeriya, ya fadi cewa ya shaidawa Sufeto Janar na ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da babbar murya cewa dole ne su hukunta maharan nan da duk wani mai hannu a ciki.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma miƙa saƙon ta’aziyarsa ga Bishop na cocin Katolika dake Enugu da kuma al’ummar Ukpabi Nimbo, bisa rashin da suka yi sakamakon hare-haren da aka kai musu.
Shugaban ya yi tsokaci a kan al’amuran kasa, inda ya tabbatar ma bishop-bishop ɗin cewa yana aiki ne a tsanake kuma yana taka-tsan-tsan domin ganin cewa ya cimma burirsa na kawo sauyi. Ya kuma tabbatar masu da cewa zai cika dukkan alƙawuran da ya daukar wa ‘yan Najeriya.
Da yake jawabi a madadin bishop-bishop din, Reverend Ignatius Kaigama ya ce, ”A shirye muke mu bai wa shugaban kasa having kai, domin muna fatan zai kawo kyakkyawan sauyi a Najeriya.”
Matsalar hare-hare da ake zargi Fulani makiyaya da kaiwa dai ta fara kamari sosai a Najeriya, inda wasu ke ganin Idan ba a tashi tsaye ba al’amarin zai iya zama wani abu daban.
The post SHUGABA MUHAMMADU BUHARI YACE YAYI UMURNI DA A LADABTAR DA MAKIYAYA appeared first on MUJALLARMU.