A kwanakin baya Jaruma Nafisa Abdullahi ta ziyarci wani kauye da ake kira Gurguzu inda ta hada kauyuka biyar ta rabar da kayan abinci a karkashin cibiyar Tallafi da ta kafa na The Love Laugh Foundation.
Tun a wannan lokacin Jarumar dai ta dauki alwashin ci gaba da tallafawa bayin Allah marasa karfi.
A cikin yunkurin da Jarumar take na ganin ta cimma burinta na tallafawa alumma,tayi kokarin hada Gagarumin taron Gidauniya wadda ta kashe makudan kudi, wadda zaa shirya ranar assabar da karfe 3 na Yamma.
Taron zai karbi bakon mahimman mutane da ya hada da Gwamnan Jahar Kaduna Malam Nasir elfurai, Sarkin Zazzau , Ali Nuhu, Umar M Shariff, Abdul M Shariff, Ali Artwork da dawo sauran Jamar da suka hada da jarumai da mawakan kudancin Najeriya.
In Sha Allah zamu halarcin taron kuma zamu kawo muku cikakken labari dan gane da taron.
The post Jaruma Nafisa Abdullahi zatayi Gagarumin taron Gidauniya domin Inganta Rayuwar Kananan Yara marasa Galihu appeared first on MUJALLARMU.