Mazauna Yankin Dansadau dake Jahar Zamfara sun bayyana irin farin cikin su da irin sojojin da aka tura musu a yankin, sunce an turo kwararrun sojoji dauke da manya manya makaman yaki.
Hakan ya biyo baya ne bayan irin ta’addancin da bayarin shanu sukeyi a yanki, domin sun kashe mutane da dama a yankin cikin yan kwanakin bayan nan da suka wuce, Sannan kuma suka yi gar kuwa da mutane 40.
Mazauna Yankin Na Dansadau suna cike da farin ciki domin kuwa suna ganin hakan zai iya taimakawa a samu cikakken tsaro a yankin. Amma suna kira ga Gwamnatin Tarayya kada tayi saurin dauke wannan sojojin da makaman yakin koda an samu shawo kan matsalar yanzu, domin kuwa hakan na iya sa su sake dawo wa kamar yadda suka yi a kwana kin baya da aka dauke sojojin da aka kawo.
The post SOJOJI SUN MAMAYE WASU YANKUNAN JAHAR ZAMFARA appeared first on MUJALLARMU.