Wani matashi mai suna Sani Hamza Funtua a garin Funtua dake a jihar Katsina, ya samu kanshi a hannun jaml’an hukumar yan sanda bayan da yayi wani rubutu akan dan majalisar jihar ta Funtua, Abubakar Muhammad Funtua.
Wata Majiya ta bayyana cewa Sani ya taba yin aiki da dan majalisar amma sai bai biya shi ba, wanda hakan ne jawo yaje a Facebook ya bayyana ma duniya.
Wata majiyar kuma ta bayyana cewa an kai Sani Hedikwatar rundunar yan sandan Jihar inda yana can a tsare a halin yanzu.
Wannan na zuwa ne bayan da yan majalisar Tarayyar suke kikarin kawo doka din rage yin amfani da kafafen sada zumunta irin su Facebook da Twitter.
The post An kama wani matashi saboda rubutu a Facebook appeared first on MUJALLARMU.