Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana godiyarsa ga majalisar dinkin duniya da sauran hukumomi dake tallawa na kasashen duniya kan taimakawa yan gudun hijrah dake a fadin kasar nan.
Shugaba Buharin, ya bayyana hakan ne a ayayin wani cin abinci da wasannin gargajiya da aka shirya domin martaba shugaban kasar kamaru Paul Biya, da matarsa Chantal Biya, ya kuma godewa jama’a da gwamnatin kamarun, da kulawarsu da yan gudun hijrah sama da dubu 56 na Najeriya tun daga shekara ta 2014.
Ana nasa jawabin Shugaba Paul Biya, ya bayyana aniyar kasarsa na kawo karshen tada kayan bayan boko haram da kuma yabawa da kokarin Shugaba Buhari, kan yaki da kungiyar a Najeriya harma da wajenta.
Daga Umar El-farooq Ahmed a Abuja.
The post SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YA BAYYANA GODIYARSA GA MAJALISAR DINKIN DUNIYA appeared first on MUJALLARMU.