Kokarin danayi wajen ganin mun shawo kan matsalar tsaro dake kalubalantar kasan nan,gwamnatin tarayya zata baiwa rundunar ‘yan sanda damar daukar sabbin jami’ai har guda 10’000 a kowacce shekara.
Inda babban sifeto ‘yan sanda Ibrahim Idris yake jawabi a wani taro na manyan jami’in ‘yan sanda a birnin tarayya abuja.
Acikin jawabin sa yayi nunin haske akan lallai ya zama dole kuma wajibi agaresu da su tashi tsaye domin ganin sun dauki mataki,domin ganin an kawo karshen miyagun laifuka a Nijeriya.
Sannan yayi kira ga majalisar dattawa ta kasa da ta gaggauta sa hannu akan kudirin da aka gabatar gareta na kara adadin kudin da ake warewa hukumar ‘yan sanda ta kasa.
The post GWAMNATIN TARAYYA ZATA FARA DAUKAR ‘YAN SANDA DUBU GOMA KO WACE SHEKARA appeared first on MUJALLARMU.