Ku karanta kuji kamar haka:-
Ya shugabana Muhammad Buhari ina maka addu’ar samun sauki da wure,sannan kadawo Nijeriya,munada bukatar da kadawo cikin koshin lafiya da walwala.
Amma zamanka a london bazai ceto kasar mu ba daga halin kuncin da ‘yan kasar ka suke ciki ba.
Kamar ziyarar da Bukala saraki da Dogara suka kaima maka a london an biya kudin tafiyar su ne daga asusun haraji na kasa wanda idan har hakan ta cigaba da faruwa to,za’a iya shiga wani hali na tangarda na tattalin arzikin kasa da kake da burin gyarawa.
Sannan Magana ta gaskiya Shugaba Muhammad Buhari ina mamakin yadda ka karfafa kwarin gwiwarka na zuwa kasar london,domin a duba lafiyarka bayan muna da kwararrun likitoci a kasar nan.
Kayi alkawarin cewa zaka za’a inganta asibitocin mu da kayan aiki na zamani kuma wadanda duniya suke amfani dasu a kasashe daban daban,domin ganin an samu kula da marasa lafiya.Amma gashi kuma kai da kanka kake fita kasar waje neman lafiya.
The post WASIKAR Dr LAZ UDE EZE ZUWA GA SHUGABA MUHAMMAD BUHARI appeared first on MUJALLARMU.