wani barawone ya ke zuwa gonan wasu tabka sata sai watarana allah yaba daya daga cikinsu damar kama shi bayan ya rike barawon sun kusa da gari sai barawo yace ma wanda ya kama shi na manta da takalmina sai mutumin yace da gaske kake barawo yace da gaske sai mutumin ya saki barawon yace dashi je ka dauko ina jiran ka barawo yace to
bayan barawo ya wuce mutumin na tsaye. yajima yana jira barawo be dawo ba sai mutumin ya wuce gida ranshi a bace yana shiga gida sai suka hadu da yayansa.
yayan nasa yace meke faruwa da kai. sai ya masa bayani yana gamawa sai yayan nasa ya kwashe shi da mari yace ya za’ayi ka kama barawo a gona kunkusa gari sai yace ma ya manta da takalminsa a gona kasake shi kace yaje ya dauko mai makon kace masa ya jiraka kaje ka dauko masa
The post GIRMA YA RIGA WAYO ZUWA appeared first on MUJALLARMU.