Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

GWAMNATIN TARAYYA ZATA BADA TALLAFIN KUDI GA MA NOMAN SHINKAFA DA ALKAMA A AREWA

$
0
0

Mataimakin Shugaban Kasa Yeme Osinbajo a jiya litinin ya ganada wasu gwamnonin arewa guda uku domin ganin yadda za’a shawo matsalar noman shinkafa da alkama a rewacin kasar nan,ta hanyar bawa manoma tallafi.

Gwamnonin da suka hada da Gwamna Abubakar bagudu (Kebbi), Gwamna Abdullahi Ganduje (Kano), Gmammna Badaru Abubakar (Jigawa).

Gwamnan jihar kebbi bagudu yayi bayanin yadda za’a inganta noman shinkafa da alkama a arewacin kasar nan ta hanyar gwamnati ta baiwa manoma tallafin kudade domin gudanar da haka.

A karshe dai gwamnatii ta yarda da wannan kudiri na bada wannan tallafi,a karkashin gwamnatin tarayya ta kasa, kuma tayi na’am da wannan tsari da aka fitar amatsayin cigaban kasa ta bangaren noma a kasar nan.

Za’a bada wannan tallafi ne ga al’ummar Nijeriya amatsayin bashi a bankuna na arewacin Nijeriya,saboda haka ga masu bukata sai suyi kokarin mallakar lambar tantancewa BVN a banki mafi kusa dakai.

marubuci:Haruna Sp Dansadau

 

The post GWAMNATIN TARAYYA ZATA BADA TALLAFIN KUDI GA MA NOMAN SHINKAFA DA ALKAMA A AREWA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>