Wasu yan bindiga sunkai wani sabon hari a kuduncin kaduna da ake kyautata zaton cewa fulani ne,a ranar lahadi da litinin da suka gabata ne inda yan sandan jahar suke bada sanarwa cewa mutane goma sha biyar sun rasa rayukan su tareda kona wasu gidaje.
Rundunar yan sanda ta kaduna tace har yanxu bata gama bincike ba akan faruwar lamarin,domin tantance mutanen da suka kai wannan hari.
Sunce dai kauyukan da harin ya shafa sun hada da Ashim Nsi da Zilan inda harin ya faru tsakanin karfe shida na safe zuwa bakai a safiya jiya liltinin a karamar hukumar GOSKA LG dake kudancin kaduna.
Mazauna garin sunce harin dai ya kashe mutane 15 ne inda kuma suka banka ma gidaje hamsin wuta,a lokacin da wani babban wakilin kauyukan yake yiwa Rundunar yan sanda jawabi,yace akan hanyarsa ta zuwa wani kauye ne yasamu labarin abubuwan dake faruwa a kauyakan biyu shi kuma nan take yayi kokarin da dawo gida domin ganin yadda lamarin yayi zafi.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
The post WASU ‘YAN BINDIGA SUN KAI SABON HARI A KUDANCIN KADUNA appeared first on MUJALLARMU.