Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

INA DA BUKATAR DOGON HUTU-INJI SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI

$
0
0

Shugaban kasa Muhammad Bhuari yace yanada bukatar dogon hutu,domin yasamu cikakkiyar kulawa akan rashin lafiyar sa,yayi wannan bayani ne daga birnin london zuwa ga fadar gwamnati.

Inda yake cewa hakikanin gaskiya rashin lafiyar sa ba wai shiri bane kamar yadda wasu suke radi raden cewa an shirya hakan ne.

Babban mai baiwa shugaban kasa shawara ta hanyar sadarwa Mr Femi Adesina yace har yanxu basu da tabbacin tsawon kwanakin da shugaban kasa zaiyi a kasar london,domin bukatar dogon hutu a akan rashin lafiyar sa da likitoci suke dubawa.

Sai dai shugaban kasa Muhammad Buhari yayi godiya ga yan Nijeriya inda yake cewa “A gaskiya Al’ummar kasa ta Nijeriya ina mika godiyata agareku ganin yadda kuke ta yawaita min addu’ar samun lafiya agareni, tundaga kan musulmai da kirista da sukyai gangami zuwa masallatai da cucina acikin kasar nan domin gudanar da addu’a ta musamman agare ni to ina godiya sosae dama sauran al’ummar Nijeriya baki daya.”

A karshe yayi kira ga yan Nijeriya da cewa su daina tada hankulan su akan rashin lafiyar sa,domin kuwa lafiya da rashin ta duk daga Allah ne sannan kuma masu yada jita jitar cewa na mutu to kusani cewa ko babu ciwo zan iya mutuwa.

Domin acikin Al’qur’ani mai tsarki Allah yana cewa

“Kulli Nafsin Za’ikatul maut,dukkanin mai rai mamaci ne.

The post INA DA BUKATAR DOGON HUTU-INJI SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>