an karbo daga afa’u daga abdullahi dan umar allah ya kara musu yarda.
shi abdullahi dan umar yace manzon allah (s.a.w) yace. wanda duk ya kwana yana me tsarki. wato yayi alwala kafin bacci.
kuma yayi bacci da alwala to wani mala’ika ze kwana a cikin mayafin sa. mutumin baze taba farkawa ba da daddare sai ya zam kowani farkawan sa wannan mala’ika yace (ya allah ka gafartawa bawanka wane)
a duk lokacin da ka farka ko kuma ka juya
sai mala’ika nan yayi maka addu’a har gari ya waye yana cewa ya allah ka gafatawa wannan bawan naka. sai ya ambaci ka da sunan da kafi so a wajan allah
dalilin wannan mala’ika shine sabo da wannan bawa wato kai ke nan dan ka kwana cikin tsarki.
ALLAHU AKBAR
wannan hadisi himmu hibban ne ya rawaito shi a cikin ingatccan littafin sa
BINCIKE
ka duba cikin himmu hibban juzi’i na uku sha’fi na dari da uku da ashirin da tara daga hadisi mai lamba ta dubu da daya
The post MAHIMMANCIN BACCI DA ALWALA appeared first on MUJALLARMU.