Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

BA’A BA BUHARI GUBA BA-INJI TSOHON DAN TAKARAR GWAMNAN JIHAR KATSINA UMAR TATA

$
0
0

Umar tata tsohon dan takarar gwamnan jihar katsina,ya gargadi yan arewa dasu daina yawan jada jita jita akan karya.

Gaskiya lamari shine shugaban kasa Muhammad Buhari ba’a bashi guba sannan kuma bai sha guba ba, kawai zance wasu yan arewa ne da suke tunanin kamar irin abinda ya faru da shuwagabannin da suka gabata kamar irin su R.murtala muhammad,Yar Adua,Sir Abubakar Tafawa Balewa da dai sauran Shuwagabannin da azzalumai suka cutar akasar nan.

Mutane da dama suna cewa ganin yadda Shugaban kasa Muhammad Buhari ya tara Makudan kudade kusan  trillion 70 yasa wasu suke tunanin bari su kasashe shi,su kwashe rabon su.

To a gaskiya bahaka bane,wannan bayani da ake cewa an bawa shugaban kasa Muhammad Buhari guba,ya fito daga bakin wani limamin masallacin juma’a ne na Yan Izala  dake Tsiga funtua Lg dake jihar katsina.

A inda yake huduba a ranar juma’a yake shaidawa al’ummar funtua cewa shugaban kasa muhammad buhari guba aka bashi,wanda kuma hakan ba gaskiya bane.

Yanzu haka dai hukumar farin kaya tana son ta gana da wannan limamin,domin taji inda ya samu wannan  labari.

Saboda haka nake kira ga yan arewa damu gujewa sharrin bakunan mu,idan bahaka zamu iya kai kan mu ga halaka .Allah ya kiyaye.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

The post BA’A BA BUHARI GUBA BA-INJI TSOHON DAN TAKARAR GWAMNAN JIHAR KATSINA UMAR TATA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>