http://mujallarmu.com/labarai/yanda-na-kama-mata-na-aisha-da-nafisa-suna-madigo/ ci gaban na farko:
Kishi ya fara kunno gidan, aka rika kai ruwa-rana. Hakan ta sanya sai da ya zage dantse wajen wanzar da zaman lafiya a gidansa. Daga bisani, kamar yadda ya ba mu labari sai komai ya lafa. Hadin kai a tsakaninsu ba kama hannun yaro.
Kafin ranar da dubun nasu ya cika, kullum sai ya rika lura cewa matan nasa kayansu iri daya. Sannan idan ranar girkin amarya ne, sai uwargida ta yi mata komai, sannan idan dare ya yi, sai ya yi da gaske zai iya kwana a dakin wadda ke girkin. Sai dai ya same ta a dakin dayar.
Sannu a hankali, ya fahimci ba sa fada a tsakaninsu, amma duk lokacin da ya shiga dakin wata, sai dayar ta rika kaiwa da kawowa a dakin har gari ya waye. Ba ya fahimtar komai! Idan kuma ya yi tafiya, duk sa’adda ya kira wayar kowacce zai fahimci tare suke, ko da cikin talatainin dare ne.
Abin ya fara damunsa don ‘ya’yansa ma aka daina kula su, sai ya dawo ya iske yara ba wanka ba wanki, ba tattalin zuwa makaranta da sauransu.
A kwana a tashi wata rana ya shirya yin tafiya sai mota ta ba shi matsala a bisa hanyarsa ta zuwa Kurmi. Tun kafin ya kai Abuja a daidai wani kuaye mai suna Katari. Da ya fahimci motar ta samu babbar matsala sai ya yanke hukuncin komawa gida, Allah bar shi da safe ya taho da masu gyara su duba motar da kyau. Ya bar yaransa a motar ya koma.
Ana ruwa kamar da bakin kwarya ya dawo, bai yi wata-wata ba, ya nufi dakin mai girki a ranar. Ya kwankwasa kamar zai balla daki, shiru, amma yana dan jin motsi a dakin. Ya koma dakin dayar, can ma shiru. Sai babban dansa ya yi firigigi ya fito. Dan kimamin shekaru 10 ya shaida masa cewa Anti Amarya na dakin mama tun dazu.
Nan fa hankalinsa ya tashi, ya nufi dakin ya sa karfi ya tura kofar. Cikin mamaki da abin da ya daga masa hankali, ya tarar da su haihuwar-uwarsu bisa gado suna yamutsa juna. Ko a jikinsu, don ba su ma san ya shigo ba.
Har sai da suka kammala abin da suke yi ne suka wartsake sannan suka fahimci mijinsu ke tsaye a kansu. Amma duk da hakan amaryar ce kadai hankalinta ya tashi, amma uwargidan ko a jikinta.
A haka aka kwana a gidan ran nan babu barci. A nan ne ya fahimci lamarin nasu ya baci. Ashe duk abin da ake yi, uwargidan ta aure masa amaryar!
To, membobin wannan majalisar da masu karatu kun ji halin da wannan bawan Allah ya samu kansa ciki. Wace irin shawara za a ba shi? A yanzu haka bai bayyana wa kowa ba sai mahaifiyarsa. Sannan bai ce da su uffan ba.
Jama’a masu mata biyu ko fiye da haka lokac ya yi da zaku rika san ya wa matan ku ido.
Jama’a Allah Ya kawo mu zamanin da kishiya ke auran kishiya.
Muna rokon Allah Ya shirya matan musulmi.
daga 1arewa.com
The post YANDA NA KAMA MATA NA AISHA DA NAFISA SUNA MADIGO – kashi na 2 appeared first on MUJALLARMU.