Babban mai gabatar da kara na gwamnatin tarayya Abubakar Malami ya ce, an dawowa da gwamantin tarayya makudan kudaden da aka sace a yakin da gwamnati ke yi da cin hanci da rashawa.
A cewar wani labari da kafara yada labarai ta PR Nigeria, Malami ya bayyana haka ne a Abuja ranar Alhamis 23 ga watan Fabrairu yayin da ya ke kare kasafin kudin ma’aikatar shari’a a gaban kwamitin shari’a da hakkin dan adam da dokoki a ginin majalisar dokoki.
Malami ya kuma ce, “Naira biliyan 50 tara ce da aka ci kamfanin MTN yayin da aka gano Naira biliyan 7 da dala miliyan 10 a gidajen wasu”.
“Sai Naira miliyan 40 da Naira miliyan 50 da aka dawo da su bisa ra’ayin kai, sai kuma wasu Dala miliyan 200, da Dala miliyan 136 da 676,000 wadanda ake shirin shigar da su asusun gwamnatin tarayya, baya ga Dala miliyan 270 wadanda aka gano su a asusun bankunan kasuwanci”.
Ko shakka babu tsabar kudi Dala miliyan 9 da 8,000 da aka kwace daga hannun tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC Andrew Yakubu na daga cikin kudaden da atoni janar din ya gano.
The post TAYA BUHARI YA GANO KUDI HAR DALA MILIYAN DARI SHIDA DA SITTIN DA SHIDA 666 appeared first on MUJALLARMU.