Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

ABIN AL’AJABI DAN SHEKARA GOMA YA KAMU DA CUTAR KANJAMAU SANADIYYAR CIN AYABA

$
0
0

Rahotanni sun nuna cewa a wani babban shagon  saida ayaba dake Wakmart na jihar Oklahoma dake kasar Amurka aka saida wannan ayabar wadda tayi sanadiyyar haifar da cutar kanjamau ga yaron.

Shafukan yanar gizo da dama sun bayyana cewar yaron ya kamu da cutar sidar ne kwanaki bakwai bayan ya ci wannan ayaban da mahaifyarsa ta siyo daga shagon na Walmart.

Rahotannin sun cigaba da fadin akwai wasu yara su takwas da suke nun ireiren alamomin nan, kuma an ce suma duk sunci wannan ayaba ne da suka siyo daga wannan katafaren shagon, an cigaba da bayyana cewar cibiyoyin gwaje gwaje sun gwada ayabar, inda suka gano cewa eh tana dauke da kwayar cutar sida.

Sai dai, ma’aikatan lafiya na kasar Amurka basu tabbatar da wannan rahoto ba, kazalika suma ma’aikatan shagon na Walmart. Bugu da kari masana sun ce kwayar cutar sida ba zata iya rayuwa idan dai ba’a jikin mutum take ba.

The post ABIN AL’AJABI DAN SHEKARA GOMA YA KAMU DA CUTAR KANJAMAU SANADIYYAR CIN AYABA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>