Mista Andrew Yakubu, tsohon shugaban kamfanin mai na kasa wato (NNPC) da ke Najeriya ya maka hukumar yaki da masu yalmundahana da arzikin kasa (EFCC) a gaban kotu, inda ya bayyana butunsa akan cewa sai Hukumar EFCC ta biya shi kimanin kudi har Naira 1,000,000,000 a samakon bata masa suna da cin zafin sa da akayi.
Andrew Yakubu ya gabatar da karar ne a wata babbar kotu da ke Abuja, wadda ta sanya ranar 9 ga watan nan domin sauraron karar.
Kudaden Da Hukumar EFCC Ta Kwace A Hannun Mista Yakubu
Mista. Adeola Adedipe Lauyan wanda ya kai hukumar EFCC kara, ya bayyana cewa Mista Yakubu da hukumar EFCC ke zargi da halarta kudaden haramun na kuma bukatar kotu ta hana hukumar ci gaba da gudanar da duk wani bincike akan sa.
A 3 ga watan Fabrairu na shekara 2017, hukumar EFCC ta kwace kudaden da suka kai kimanin dalla $10,000,000 a gidan Mista Yakubu wanda ake zargi da halarta kudaden haramun, a gidan shi da ke Sabon Tasha da ke Kaduna.
The post MISTA ANDREW YAKUBU YA MAKA EFCC KOTU appeared first on MUJALLARMU.