Rahotanni sun bayyana cewa wasu malaman makaranta dake karantarwa a wata firamari dake karamar hukumar Cross River mai suna Biase sun koma sana’ar gadi.
Ciyaman dake wakilcin yankin maisuna Dr Steven Odey yace idan har mutum yana so yazama malami mai kwazo to sai yaje makaranta,domin jajircewa wajen karatu sannan da fahimtar abinda yaje koyo,domin samun sakamako mai kyau.
Su dai wadannan malaman guda sha daya 11 sunce dalilin dayasa suka koma sana’ar gadi shine:- saboda albashin da zai zo masu a wata ba zai iya wadatar dasu komi ba.
Dr Steven Odey ya kara da cewa har yanxu gwamnatin Cross River din dai bata tsaida takamaimar magana ba akan yanki adadin nawa za’a rinka biya malaman firamari albashi ba,amma ana saran nan bada jimawa ba komai zai daidai ta.
The post MALAMAN MAKARANTA SHA 11 SUN KOMA SANA’AR GADI A CROSS RIVER appeared first on MUJALLARMU.