Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

HANYOYI 5 DA ZAKA BI KA GYARA WAYARKA DA KANKA IDAN TA FADA RUWA BA SAI KA KAI GYARA BA

$
0
0

Idan har wayar ka/ki ta fada ruwa bawai ana nupin ta tashi aiki kenan ba,a’a za ka/ki bi wasu hanyoyi ne domin ganin ta dawo dai dai kamar haka:-

  1. KADA DANNA KOMI BAYAN KA TSAMU TA DAGA CIKIN RUWA                                   abu na farko da zakayi kokarin yi shine ba.a bukatar ka girgiza wayar  ko kayi kokarin danna wani key ko kuma kayi kokarin sharce ruwan dake jikinta idan kai mai tunani ne,idan har kana son wayar ta tsira.
  2. KA BUDE BAYAN WAYAR KA CIRE BATIR                                                                        abu na gaba da zakayi shine bayan ka ciro wayar daga cikin ruwa,to sai kayi hanzarin cire batir din ta
  3. KA CIRE SAURAN ABUBUWAN DA SUKA SHAFI LAYI DA MEMORY CARD             abu na gaba kamar wadanda batir din wayar su ba’a cire sa,to abinda ake bukatar suyi shine su cire layukan dake jikin wayar tareda da memory card
  4. KA SHANYA WAYAR ACIKIN RANA TA BUSHE KO KUMA KAYI AMFANI DA FANKA                                                                                                                   mataki na hudu ana son ka shanya wayar acikin rana domin tasamu bushewa sosae ya zama babu koda digon wani ruwa ko lema acikin ta,sannan sai ka kunna wayar,to da yardar Allah wayarka zata dawo dai kamar bata taba fadawa ruwa ba,idan kuma bata kunnu ba to sai ka sata  a caji,idan nan ma bata kawo wuta ba to sai ka ajiye ta na zuwa kwana daya ko biyu sannan sai kazo ka kara kunnata to insha Allahu wayarka zata dawo normal.
  5. BAYAN KWANA DAYA KO BIYU IDAN BATA KAWO BA ZAKA IYA KAITA WAJEN MAI GYARA WANDA KA TABBATAR DAYA IYA GYARA SOSAI                                 mataki na karshe shine bayan duk ka cika sharuda hudun bata kawo wuta ba,to sai ka dauketa ka kai wajen mai gyara wanda ka tabbatar da kwarewarsa a fannin gyara domin ya dumama maka ita da hita ta waya,amma zai cajeka wasu yan kobbai.amma kada ka sake kaba kowa wayarka idan ba engineer ba.

 

 

 

 

The post HANYOYI 5 DA ZAKA BI KA GYARA WAYARKA DA KANKA IDAN TA FADA RUWA BA SAI KA KAI GYARA BA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050