Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

DALILAI 5 DA KESA MACE TA FITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA

$
0
0

ABUBUWAN DA KE SA MACE TA FITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA SUNA DA YAWA, AMMA GA KADAN DAGA CIKIN WADANNAN ABUBUWAN

RIKO: Riko shine idan mijinki ya aikata wani  laifi, kibar abin a zuciyar ki ba tare da yafiya ba, yana da hadari kwarai da gaske. Duk sanda namiji ya yi miki wani abu yana sani ko bai sani ba to ki samu wani lokaci da yake cikin nutsuwa ko yake cikin nishadi ki nuna masa cikin tausasa harshe misali “wane kayi min kaza nasan in Allah ya yarda zai dau kuskuren shi kuma za ki kuma shiga zuciyar shi

YAWAN MITA: Duk macen da take da yawan mita in anyi abu baya wucewa to zata dinga sanewa maigidanta kuma bata fiya darajaba

FUSHI: Duk mace mai yawan fushi idan sun dan samu sabani da maigida mafi yawanci da namiji idan kuka sami dan sabani in ya fita ya manta kika cigaba da yin fushi ko ya dawo  yana sa mace ta fita daga zuciyar namiji yana da kyau yar uwa ki dunga kai zuciyarki nesa

RASHIN IYA GIRKI: Girki, wani ginshiki ne na sinadarin zaman aure rashin iya shi yana kawo matsala tsakanin maigida da uwar gida in dai har baya samun jindadin abincin da uwargida ke yi har yaji abincin da zaici na waje yafi na gida dadi matsala ta faru domin yana ragewa uwargida daraja, iya girki yana sa maigida yaso uwargidansa idan maigida ya wadata iyalinsa da abinci to yakamata uwargida ta tsaya tsayin daka wajan ganin ta iya salo -salo na tasarinfin abinci
A hakikanin gaskiya tattalin arziki yana tasiri wajan wadata komai to amma bahaushe yace da ruwan ciki wai ake jan na rijiya don haka yar uwa in dai har zaki kula da abin da maigida zai ci ba wai kullum abu daya ba ki kasance ko wane fanni na girki kin kware akwai marubuta da sukayi kokarin rubuta littafan koyon girke girke yana da kyau uwargida ta nazarci irin wadannan littafan don koyon salo salo na girki
duk sanda maigida ya dawo zai tarar kin gama komai na abinci sannan akwai wani sirri na girki da yawanci maigidanta suka fi so shine
duk sanda yar uwa ta kawowa maigida abinci ta zauna a gabanshi yana ci kina yi mishi hira mai dadi rashin haka yana sawa mace ta fita daga zuciyar namiji

RASHIN BAWA MAIGIDA HAKKINSA: Rashin biyawa maigida bukatarshi wajen kwanciya illah ce babba da take kawo tabarbarewar aure duk sanda maidiga zai neme ki za ki yi raki ko ki tsaya jin kunyarshi yana sa mace ta fita daga zuciyar maigida amma in har mace zata zama mai jure bukatar mijinta tare da rashin gajiyawa ko tana so ko bata so karta yadda ya gane ko da tana cikin halin (period) ne akwai hanyoyi da dama da zata gamsar da shi.

The post DALILAI 5 DA KESA MACE TA FITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>