Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

BARCELONA TA DOKE PSG DA CI 6 DA 1

$
0
0

ani abu da duniyan kwallon kafa za ta dade tana tattauna batunsa shi ne yadda kungiyar Barcelon ta farka daga gyangyadin da ta yi makwanni biyu da suka shige inda ta sha kasi a hannu takwararta ta PSG da ci 4 da nema a wasan neman shiga zagaye na 8 na gasar cin kofin zakarun turai da aka yi bugawar farko a gidan PSG din

Sai dai wani abin mamaki shi ne a wannan dare Barcelona ta casa PSG da ci 6 da1 a gidanta wasa ya tashi 6 da 5

Barcelon ta fara wasan na wannan dare cike da karsashi ba kamar wasan farko ba inda kafin ka ce me sun jefa kwallaye uku a ragar PSG

Edison Cavani na PSG ya fadar da gaban magoya bayan Barcelona bayan da ya zura kwallo a ragar Barcelona

Sai dai ‘yan wasan na Barcelona ba su karaya ba, sun ci gaba da murza leda da kwarin gwiwa wanda shi ne ya basu damar ci gaba da zura kwallaye har a mintin karshe na wasan, wanda hakan ya basu damar fidda PSG daga gasar ta bana

The post BARCELONA TA DOKE PSG DA CI 6 DA 1 appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>