Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

HUKUMAR EFCC TA GURFANAR DA WANI BOKA A KOTU AKAN DAMFARAR KUDI NAIRA MILIYAN 5.6

$
0
0

A ranan Talata, 7 ga watan Maris, Hukumar Hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da wani boka mai suna Clement Joseph alias Dr. Omale gaban alkali Jastis A. Otaluka.

Game da cewa kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, bokan na fuskantar laifuka 7 wanda ya kunshi yaudara da damfaran na kudi N5.6 million.

Shi da abokan yaudaran shi wadanda suka arce sun damfari wata mace mai suna Bola Akintola da sunan cewa zasu tsiratar da ita daga mutuwan fuji’a.

Jawabin yace:

“ Clement Joseph (Alias Dr. Omale), Mr. Paul , Mr. Papa , Mr. Ifeanyi da Mrs Ments a ranan 26 ga watan Yunin 2016 sun amshi kudi miliyan 1 daga hannun Mrs Bola Akintola akan cewa ku bokaye ne kuma kun amshi kudin domin tsubbu na hanata mutuwan fuji’a.

Alkali Jastis Otaluka ya dakatad da karar zuwa ranan 23 ga watan Maris domin fara ainihin gurfana.

The post HUKUMAR EFCC TA GURFANAR DA WANI BOKA A KOTU AKAN DAMFARAR KUDI NAIRA MILIYAN 5.6 appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>