Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

BUHARI ZE KOMA ASIBITI

$
0
0

Shugaban  Muhammadu Buhari ya ce yana samun sauki sosai kan rashin lafiyar da ke damunsa, “amma watakila nan da makonni kadan masu zuwan zan koma asibiti”.

Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa ‘yan kasar a fadarsa da ke Abuja jim kadan bayan saukarsa daga birnin London, inda ya kwashe kusan wata biyu yana hutu da kuma jinya.

A cewarsa, bai taba kwantawa rashin lafiya irin wacce yake fama da ita yanzu ba.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, “Ina matukar nuna godiya ga dukkan ‘yan Najeriya, Musulmi da Kirista, wadanda suka yi ta yi min addu’a, kuma suke ci gaba da yi min addu’ar samun sauki”.

Shugaban na Najeriya ya ce babban abin da zai sanya a gaba yanzu shi ne yi wa ‘yan kasar aiki tukuru domin bayyana musu irin jin dadin da ya yi da addu’o’in da suka yi masa.

The post BUHARI ZE KOMA ASIBITI appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>