Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

LABARI CIKIN HOTUNA KUNGIYOYIN MUTANE 5 BIYAR NE BASU MURNAR DAWOWAR SHUGABA BUHARI GIDA NIJERIYA

$
0
0

A yau ne dai shugaban kasa Muhammad Buhari ya dawo gida Nijeriya daga kasar landan,inda ya kwashe kimanin kwanaki hamsin acan domin a duba lafiyar sa.

Mutane da dama suna hasashen cewa kungiyoyu guda biyar ne basu kaunar shugaba Buhari ya dawo gida,sannan kuma basu murnanr dawowar sa.

Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya

Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya

Duk dayake al’umma da dama na farin ciki da dawowar shugaba Buhari, kuma zaka gane haka daga shafukan yanar gizo inda jama’a da dama ke bayyana farin cikinsu da yi ma shugaban fatan alheri, yayin da da kuma wasu ke zuba ruwa a kasa suna sha, wasu kuma ke hada taron gangamin nuna farin ciki a garuruwa daban daban.

Sai dai duk da haka akwai wasu kason yan Najeriya da ko kadan basa farin ciki da dawowar shugaba Muhammadu Buhari gida Najeriya. Cikinsu akwai:

Tun bayan tafiyar shugaba Buhari ne dai jam’iyyar PDP ta fara caccakar gwamnatinsa da shi kansa, inda har daga cikinsu suka dinga kiraye kirayen da yayi murabus, wasu kuma suka dinga yada jita jitan wai ya mutu. Don haka dawowarsa cikin koshin lafiya yayi matukar razana su.

2. IPOB

Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya

Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya

3. Yan Shia’a

Da shugaba Buhari ya fara dadewa a kasar Birtaniya bayan tafiyansa, sai yan shi’a suka fara watsa labaran karya wai cewa ai tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mutu, inda wasu daga cikinsu suke rantsewa da Allah cewa lallai Buhari ya mutu, har ma an samu wata mata da tace muddin Buhari ya dawo ta bar addinin Shi’a. toh yanzu da Buhari ya dawo bamu san halin da zasu shiga ba.

Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya

Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya

Haka zalika suma kungiyar MASSOB dake da manufa iri daya da IPOB na fafutukan samar da kasar Biafra zasu yi bakin ciki da dawowar shugaba Buhari Najeriya, saboda sun nuna ba’a tare da shugaban tun da fari.

5. Barayin gwamnati

Yaki da cin hanci da rashawa da shugaba Buhari yake yi a kasar ta girgiza barayin gwamnati da dama a kasar nan, don haka dayawa daga cikin ire iren barayin nan ba zasu taba yin fatan Buhari ya dawo gida Najeriya ba.

 

The post LABARI CIKIN HOTUNA KUNGIYOYIN MUTANE 5 BIYAR NE BASU MURNAR DAWOWAR SHUGABA BUHARI GIDA NIJERIYA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>