Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

BAN TABA MAKAMANCEWAR RASHIN LAFIYAR DA NAYI A WANNAN LOKACI BA-SHUGABA BUHARI

$
0
0

– Shugaba Buhari a jiya da safe bayan dawowar sa daga kasar Ingila domin jinya ya shaidawa mutanen dake kusa da shi cewar bai taba yin irin rashin lafiyar da yayi ba a wannan karon.

– Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wasu jiga-jigan jam’iyyar sa da kuma jami’an gwamnati a fadar shugaban kasar.

Ban taba irin wannan mummunar rashin lafiyar ba - Buhari

Ban taba irin wannan mummunar rashin lafiyar ba – Buhari

A jiya ne dai Labaran da muke samu yanzu yanzu suna nuni da cewa garin Daura dake zaman mahaifar Shugaba Buhari ya kaure murana sakamakon dawowar shugaban da safiyar yau.

An dai dandazon jama’ar garin da ma masoya da dama daga makobtan garin sun yi dandazo a filin sukuwar garin dake gaban fadar sarkin na garin dama sauran manyan tituna na garin.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya a ranar Juma’a da misalin karfe 4 na safe, bayan kwanaki 49 da barin kasar don hutun ganin likita.

A cewar jaridar Thisday, sakamakon rufe filin jirgin saman Abuja an shirya saukar jirgin sa a filin jirgin Kaduna a safiyar ranar Juma’a, bayan shawarar da aka yanke na dawo dashi a jirgi mai saukar ungulu zuwa fadar shugaban kasa, Abuja.

The post BAN TABA MAKAMANCEWAR RASHIN LAFIYAR DA NAYI A WANNAN LOKACI BA-SHUGABA BUHARI appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>