Hukumar Zaben Najeriya INEC, ta sanya ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2019 a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘Yan Majalisun Tarayya.
Sanarwar da hukumar ta fitar ta nuna cewar za a gudanar da zaben Gwamnoni da na ‘Yan Majalisun Jihohi a ranar 2 ga watan Maris.
Hukumar ta kuma sanar da cewar ta dora jami’an ta 23 da ake tuhuma a kotu da laifin magudin zabe kan rabin albashi har sai an kammala shari’ar da ake yi musu.
INEC ta dai bai wa ‘yan Najeriya tabbacin gudanar da zaben cikin tsari tare da daukan mataki kan duk wani jami’inta da aka samu da aikata laifin karya dokokin zabe.
The post INEC TA SANAR DA RANAR DA ZA AYI ZABAN 2019 appeared first on MUJALLARMU.