Yan Kungiyar CAN sun ce sun ga canji da zuwan shugaban kasa Buhari
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
CAN ta Jihar Borno ta yabawa Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kwanan nan ne Kiristoci suka yi bikin ‘Easter’ Kiristocin Borno sun yabawa Gwamnatin Buhari
CAN ta yabawa kokarin Sojojin Najeriya masu yaki da ta’addancin Boko Haram. CAN din ta jinjinawa irin kokarin da Sojojin kasar suka yi wajen fada da ‘Yan Boko Haram.
Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa Kiristocin Jihar Borno sun bayyana cewa bana sun yi bukukuwan ‘Easter’ da aka saba cikin kwanciyar hankali.
Kiristocin Borno suka ce an dade rabon da su samu kwanciyar hankali irin wannan karo.
Bishof Mohammed Naga wanda shi ne shugaban Kungiyar Kiristoci watau CAN yayi wannan bayani a wani taro da aka yi.
Bana dai an yi bikin ‘Easter’ ba tare da wani takunkumi ko fitinar Boko Haram ba a Jihar Borno.
The post KUNGIYAR KIRISTOCI (CAN) DAKE JIHAR BORNO SUN YABAWA MULKIN SHUGABA BUHARI appeared first on MUJALLARMU.