Jaruma Hadiza Gabon ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta yi aure ba.
A wata hira da ta yi da kafar yada labarai na BBC, Hadiza Gabon ta fadi cewa duk da ta na son ta yi aure, hakan ba zai samu ba har sai lokaci ya yi.
A fadar ta “Wallahi babu wata mace da za ta so ta kai lokacin aure amma ta ki yi”, sai dai ta ce auren kamar mutuwa ya ke kuma lokaci ne, idan har lokaci ya yi babu yadda mutum zai guje masa.
Jarumar dai ita ta lashe lambar yabo na ‘yar wasan da ta fi tallafawa babban jarumi a fim a bikin bayarda kyaututtuka na ‘Africa Films Awards’ na bana.
Hadiza ta ce tana kaunar dukkanin masoyanta kuma tana kira garesu da su yi mata addu’a.
daga alummata.com