Kina da kima da mstsayi da daraja da mutunci da kwarjini da tarin falala,
ina sonki kuma ina kaunarki wanda babu adadi. Matsayinki da martabarki ta yi nisa sosai sama da tazarar sama da kasa. Allah ya fifita ki da martabobi masu dimbin yawa.
Rayuwarki ta anfanar da
al’umma sama da anfanin abinci a gangar jikin dan Adam. Ke uwace ta duk wani bawa na kwarai da yake bin Manzon Allah (s.a.w ) babu wanda zai
so ki sai mumini, babu wanda zai zage ki ya yi miki kazafi, sai wanda bashi da
rabo a duniya da lahira.
Ke ce wadda Allah ya barrantar daga sama, duk wanda ya aibataki bayan
Allah ya barrantar da ke, to bada kowa yake jayayya ba sai da Allah. Ke ce wadda Manzon Alllah ya fi so, shi
kuma baya son komai sai abin da Allah yake so, don haka ke zabin Allah ce ga
Manzonsa.
A dakinki Allah ya karbi
Mansonsa kuma yana tsakanin kirjinki da habarki, kai kina da tarin falala uwar muminai.
Shin hankali lafiyayye wanda bai gurbata da hahinci da shubuhohi da munafunci ba zai yarda
da cewa ke ba tagari ba ce. Babu wanda zai yarda sai tababbe mai tababben hankali.
Mai karatu!!! ka san wace ce wannan kuwa? Ita ce Nana Aishatu matar Manzon Allah Duniya da Lahira ‘yar Abubakar
Siddik sonta Imani, zaginta kafirci da fada da Allah da Manzonsa.
Allah ya dauki ranmu muna masu kaunar uwar
muminai. Amin
Ustaz Nuhu Ubale Ibrahim
(Abu Abdilhalim)
Talata: 22/11/2016.
The post KINA DA KIMA SOSAI appeared first on MUJALLARMU.