Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

YADDA AKE SHIRIN KWANCIYAR BARCI

$
0
0

Idan kazo zaka kwanta barci, farkon abinda zaka
fara yi shine Alwala. kaje kayi tsarki sannan kayi
alwalar.
2. Idan baka yi shafa’i da Wutri ba, sai ka yisu.
amma idan kana tsammanin ba zaka makara ba,
zaka iya barinsu sai chan karshen dare kafin
hudowar alfijir.
3. Kayi ma kanka hisabi. ka tuno da laifukan da ka
aikata tun daga wayewar gari zuwa yanzu. ka yi
nadama ka nemi gafarar Allah bisa laifukanka.
sannan ka rokeshi ya karba maka ayyukanka na
alkhairi.
4. Ka karanta SAYYIDUL ISTIGFAR. domin kuwa
Manzon Allah (saww) yace duk wanda ya
karantashi da yamma (ko dare) in dai ya mutu
awannan daren to shi ‘dan Aljannah ne.
6. Ka karanta Ayatul kursiyyi domin neman tsari
daga sharrin kowanne shaitani na fili da na boye.
Manzon Allah (saww) yace idan ka karanta Ayatul
kursiyyi yayin da zaka kwanta barci, to Allah zai
sanya Mala’ikansa ya rika tsaronka. har wayewar
gari babu wani shaitanin da zai kusantoka.
7. Ka karanta Qul-huwallahu 3, da Falaki da Nasi
uku-uku. ka tofa ahannayenka kana shafewa jikinka
dashi. Haka Manzon Allah (saww) yake yi.
8. BISMIKAL LAHUMMA AMUTU WA AHYA (Manzon
Allah saww yana karanta haka kafin ya kwanta).
9. Ka kwanta akan gefenka na dama, ka kalli
alqiblah in da hali.
10. Allahumma Qinee Azabaka yauma tab’athu
Ibadaka (3) – Ita ma Manzo (saww) yana yinta
yayin da ya kwanta bisa shimfidarsa.
11. Kaci gaba da yin Salati da Manzon Allah
(saww) har barci ya kwasheka.
Addu’o’in kwanciyar barci suna da yawa sosai

The post YADDA AKE SHIRIN KWANCIYAR BARCI appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>