Gwamnan jahar borno kashim shettima kamar yadda muke samun bayanai da kauyuka daban daban na jihar,suna nuni da cewa akasarin mutane 100,000 suka rasa rayukansu ta sanadiyyar rikicin boko haram a jihar ta borno.
Alhaji Kashim Shettima yayi wannan zance ne awajen taron tunawa da mazan jiya marigayi janar Murtalaa Muhammad,da aka gudanar a dakin taro na tunawa da Shehu Musa Yar Adua dake abuja a inda yake bayani akan irin ta’asar da yan boko haram sukayi a jihar ta borno.
Ya kara da cewa sama da mutane miliyan biyu ne suka rasa gidajen su a sakamakon ta’addancin boko haram,sannan mutane 537,815 suna zama a sansanonin yan gudun hijira dake jihar,wasu kuma suna zaune ne a kauyuka mafi kusa da gari.
The post AKALLA AKWAI ZAWARAWA 54,911 A JIHAR BORNO-INJI GWAMNA SHETTIMA appeared first on MUJALLARMU.