Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na shirin kaddamar da kwalejin horarwa ta kwallon kafa a Legas, birni mafi girma kuma cibiyar kasuwancin Najeriya.
Kwalejin wadda za ta zama irinta ta farko a nahiyar Afirka, za a tafiyar da ita bisa tsarin babbar kwalejin kungiyar ta ‘La Masia Academy’ da ke kasar Sifaniya.
Ita dai wannan babbar kwalejin ta samar da fitattun ‘yan wasa kamar Andres Iniesta da Lionel Messi da kuma Xavi.
Sabuwar kwalejin ta Najeriya da aka yi wa lakabi da ‘f.c.b scola Lagos’, za ta zauna ne na wicin-gadi a filin wasa na Teslim Balogun da ke unguwar Surulere, a birnin na Legas.
Abun da za ka fara hange da ka shiga kwalejin shi ne katafaren hoton dan wasan kungiyar na tsakiya wato Iniesta.
Sannan kuma an sanya hotunan fitattun ‘yan wasan kungiyar kamar Lionel Messi da Luis Suarez da kuma Neymar, a kan allunan tallace-tallace.
Ana horar da kananan yara masu shekara biyar zuwa 18, yadda tamaula take a mahangar kungiyar Barcelona.
Yanzu haka akwai yaran da suke biya domin samun horaswa kamar guda 400, a inda suke biyan $600, a kowace shekara.
Suna daukar darasi kamar sau daya a mako.
Kuma kusan za a iya cewa burin kowane daya daga cikin daliban bai wuce samun damar zuwa babbar kwalejin Barcelona ta ‘La Masia Academy’ da ke kasar Sifaniya.
The post DA ALAMUN ZA A SAMU DAN KWALLON KAFA SAMA DA MESSI A NAJERIYA appeared first on MUJALLARMU.